Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-03-23 09:16:05    
Ciwon sankarau ya kashe mutane 40 a kasar Kodivwa

cri

Ran 22 ga wata, wani jami'in kungiyar kiwon lafiya ta kasashen duniya wato WHO wanda ke aiki a kasar Kodivwa ya tabbatar da cewa, tun daga farkon shekarar nan, a birnin Bouna da ke arewa maso gabashin kasar Kodivwa, mutane fiye da 200 sun kamu da ciwon sankarau, kuma 40 daga cikinsu sun riga sun mutu.

Jami'in na kungiyar WHO ya nuna cewa, birnin Bouna na karkashin tutar dakaru masu 'yancin kai wadanda suka yi adawa da gwamnati a da, shi ya sa babu isasshen maganin rigakafi da likitoci a wurin, wannan ya haddasa barbazuwar annobar. Kungiyar WHO ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su hanzarta su bayar da maganin rigakafi ga wurin.(Bello)