Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-03-22 16:44:05    
Kasar Congo(Kinshasa) ta kirawo 'yan wasanta na kwallon kafa don shirya muhimman gasanni 2 masu zuwa

cri
Ministan harkokin wasanni da matasa na kasar Congo(Kinshasa) ya ba da sanarwa a ran 21 ga wannan wata cewa, kungiyar wasan kwallon kafa ta kasarsa za ta kirawo 'yan wasanta na kwallon kafa su 17 wadanda suke aiki a kasashen waje don shirya gasar cin kofin Afirka ta wasan kwallon kafa wato gasar share fage domin gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa mai zuwa.

Kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Congo(Kinshasa) za ta yi takara da kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Ghana a birnin Kinshasa, hedkwatar kasar a ran 27 ga wannan wata. Yanzu kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Congo(Kinshasa) tana yin shiri a kasashen Turai, inda ta taba lashe kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Cote d'Ivoire a cikin gasar motsa jiki da aka yi a kasar Faransa.(Tasallah)