Ran 21 ga wata, Mr Hifikepunye Pohamba mai shekaru 69 da haihuwa wanda ya ci zaben zaman shugaban kasar Nimibiya ya yi rantsuwar hawa kujerar mulkin kasar a birnin Windhoek, hedkwatar kasar, nan take ya zama shugaban kasar na biyu tun bayan samun 'yancin kan kasar Nimibiya a shekarar 1990 bayan tsohon shugaba Sam Nujoma.
An yi bikin rantsar da shugaba Pohamba ne a wani filin wasannin mota jiki na birnin Windhoek. Shugaban kasar Afrika ta Kudu Thabo Mbeki da takwaransa na Zimbabwe Robert Mugabe da sauran shugabannin kasashen Afrika da dama da kuma jama'ar Namibiya wanda yawansu ya wuce dubu 20 sun halarci bikin.
A ran nan kuma Mr. Pohamba ya bayar da sanarwa kan sunayen 'yan majalisar ministoci ta kasar, wato Nahas Angula ya zama firayim ministan kasar, da Libertine Amathila ya zama mataimakin firayim ministan kasar, da kuma Marco Hausiku ya zaman ministan harkokin waje.(Kande Gao)
|