Shugaban gwamnatin wucin gadi ta kasar Guinea Bissau Mr. Rosa ya yi jawabi ta gidan rediyo a ran 21 ga watan nan a birnin Bissau, babban birnin kasar, cewa za a jinkirtar da lokacin zaben shugaban kasar Guniea Bissau wanda aka tsai da yinsa a watan Mayu na shekarar nan har zuwa watan Yuni na shekarar da muke ciki.
Kuma Mr. Rosa ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu ba a gamsu da wasu ayyukan shirya zaben nan ba, shi ya sa za a jinkirta da yinsa.
Bisa labarin da muka samu, an ce, ban da babbar jam'iyyar 'yan hamayya wadda ake kiranta sabuwar jam'iyyar juyin juya hali da kuma jam'iyyu biyu da suka ki yarda da wannan, dukkan sauran jam'iyyu sun yarda da jinkirta da lokacin zaben.(Kande Gao)
|