Ran 21 ga wata, a birnin Kinshasa, mai magana da yawun rukunin musamman na MDD da ke kasar Kongo Kinshasa ya nuna wa maneman labaru cewa, yanzu sojoji farar hula na kabilun yankin Ituri da ke arewa maso gabashin kasar Kongo Kinshasa sun sa hanzari ga aikin kwance damara.
Bisa cewar kakakin nan, sojoji farar hula na kabilu fiye da 4100 sun gabatar da makamai su da kansu a ran 20 ga wata. Nan gaba, a ko wace rana, rukunin musamman na MDD zai ba da taimako ga sojoji farar hula 100 domin su kwance damara, su koma zamantakewar al'umma.
Ban da wannan kuma, a ran 21 ga wata, rukunin musamman ya bayar da wata sanarwa, inda aka nuna fatan cewa, za a shawo kan kungiyoyin sojoji farar hula 6 na yankin Ituri da su kwance damara cikin sauri.(Bello)
|