 Kugniyar musamman ta Majalisar Dinkin Duniya da ke kasar Congo(Kinshasa) ta ba da sanarwa a ran 17 ga watan nan cewa, a ran 16 ga wannan wata sojojin kiyaye zaman lafiya sun dauki matakan soja a yankin Ituri da ke arewa maso gabashin kasar, don tsorata sojoji farar hula na kabilu wadanda suka ki kwance damara, wannan ne karo na 3 da sojojin kiyaye zaman lafiya suka dauki matakan soja tun daga farkon wannan wata.
Wannan sanarwa ta kara da cewa, sojojin kiyaye zaman lafiya fiye da dari 5 sun yi maci zuwa wani kauye mai suna Zombe na yankin Ituri, inda ake zaton cewa, dakarun farar hula wadanda ake tuhumarsu da laifin kai wa sojojin kiyaye zaman lafiya 'yan kasar Bangladesh hari a ran 25 ga watan Fabrairu suna buya a ciki. Sojojin kiyaye zaman lafiya ba su yi dauki ba dadi da sojojin farar hula na wurin ba, amma sun kwace wasu makamai da harsashi.(Tasallah)
|