Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-03-17 10:39:15    
Kawancen Kasashen Afirka zai tura sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa yankin gabashin kasar Congo(Kinshasa)

cri
Jami'in musamman na kwamitin zaman lafiya da tsaron kai na Kawancen Kasashen Afirka Said Djinnit ya ba da sanarwa a birnin Addis Ababa, hedkwatar kasar Habasha a ran 16 ga watan nan cewa, kawancensa zai tura sojojin kiyaye zaman lafiya kimanin dubu 7 zuwa yankin gabashin kasar Congo(Kinshasa) don ba da taimako wajen komar da sojojin tsohuwar gwamnatin kabilar Hutu ta kasar Rwanda da dakarun farar hula na kasar Rwanda wadanda suke buya a kasar Habasha.

An bayar da wannan sanarwa ce bayan da aka rufe taron da kwamitin nan ya yi kwanaki 2 yana yi a cikin asiri kan halin da kasar Congo(Kinshasa) take ciki. Ban da wannan kuma, sanarwar nan ta yi kira ga wadannan sojojin tsohuwar gwamnatin kasar Rwanda da dakarun farar hula da su kwance damara tun da wuri, kuma su fara zaman rayuwarsu yadda ya kamata. Sa'an nan kuma, wannan sanarwa ta yi gargadi ga wadannan sojoji da dakarun farar hula cewa, idan ba su koma kasarsu da kansu ba, to, za a tilasta musu da karfin soja.(Tasallah)