Ran 16 ga wata, a birnin Monrovia, fadar mulkin kasar Liberia, Jacques Klein, wakilin musamman na MDD kan maganar Liberia ya bayar da wata sanarwa, inda ya yi nuni da cewa, kungiyar musamman da ke aiwatar da aikin kiyaye zaman lafiya a kasar Liberia za ta dauki matakin, yadda za a shawo kan tarzomar da ka iya bulla a kasar.
Kwanakin baya, wasu dakarun da ba sa ga maciji da gwamnatin kasar sun yi barazanar yin tarnaki ga aikin wanzar da zaman lafiya domin rashin jin dadin cire mukamin George Dweh, shugaban majalisar dokoki ta wucin gadi da aka yi. A kan haka ne, Mista Klein ya yi jawabinsa, inda ya yi gargadin cewa, sojojin wanzar da zaman lafiya da ke kasar Liberia za su yi kokari domin kiyaye kwanciyar hankali a zamantakewar al'ummar kasar da kare aikin shimfida zaman lafiya a kasar, da kuma hana bullowar al'amarin nuna karfin tuwo. (Bello)
|