A ran 16 ga wata shugaban jihar Kasai Occidental na kasar Kongo(Kinshasa) Clement Kantu ya bayyana cewa, a kwanakin nan, an sami gocewar kasa cikin wani ramin haka lu'ulu'u na jihar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 40.
Bisa labarin da muka samu, an ce, wannan rami yana iyakar kasa da ke tsakanin kasashen Kongo(Kinshasa) da Angola, kuma an yi hadarin ne a karshen watan Fabrairu na wannan shekara, sabo da na'urorin sadarwa da zirga-zirga su ba na zamani ba ne, shi ya sa bayan da aka yi hadarin da rabin wata, sa'an nan mutanen da ke birnin Kinshasa, babban birnin kasar sun sami labarin. Bisa labarin da muka samu, an ce, an yi wannan hadari ne a sakamakon hakar lu'ulu'u da aka yi ba bisa doka ba.(Danladi)
|