Gwamnatin kasar Tanzania ta riga ta tsara shirin rage ko soke wasu harajin ayyukan noma domin kara raya sha'anin noma wanda ya fi muhimmanci a kasar.
Jaridar wannan kasa da aka fi sani da suna The African ce ta tsamo maganar karamin ministan fadar shugaban kasar Abdallah Kigoda wanda ya bayar da wannan labari a ran 16 ga wata.
Mr. Kigoda ya ce, bayan an rage ko soke wasu harajin sha'anin noma, za a iya rage tsadar wasu kayayyakin amfanin gona. Yawancin kudin waje da kasar Tanzania ke samu tana samu ne daga sha'anin noma, kuma yawancin mutanen kasar suna aiki a filayen noma wanda ya fi sauran fanonnin tattalin arziki muhimmanci a kasar.
Bisa shirin rage wasu harajin sha'anin noma da za a gabatar da shi zuwa ma'aikatar kudi ta kasar don shekarar kasafin kudi daga shekarar 2005 zuwa shekarar 2006. Bisa shirin nan, za a soke harajin da aka nema lokacin da ake yin sufurin kayayyakin amfanin gona da harajin kwastan na kayayyakin amfanin gona kuma da harajin da suke shafar injunan noma. (Sanusi Chen)
|