A 'yan kwanakin nan annobar sankarau tana yaduwa sosai a yankin arewa maso gababashin kasar Cote dI'voire, wadda har ta yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 30 da suka kamu da ciwon. Sabo da haka, kungiyar kiwon lafiya ta kasa da kasa tana mai da hankali sosai kan wannan.
A ran 15 ga wata, ofishin wakilin kungiyar kiwon lafiya ta kasa da kasa da ke kasar Cote dI'voire ya tabbatar da cewa, a yankin Bunna na kasar Cote dI'voire da ke iyaka da kasar Burkina Faso an riga an gano masu ciwon sankarau 168. Mutane 37 daga cikinsu sun riga sun mutu. Sabo da haka, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Cote dI'voire tana da shirin tura wasu likitoci zuwa yankin domin yin rigakafi da hana yaduwar annobar ciwon. (Sanusi Chen)
|