
Shugadan Nijeriya Olusegun Obasanjo Ministan harkokin wajen kasar Nijeriya Olu Adeniji ya bayyana a birnin Abuja, hedkwatar kasar a ran 16 ga wannan wata cewa, kasarsa za ta ci gaba da neman samun kujerar din din din ta kwamitin sulhu ta Majalisar Dinkin Duniya.
Mr. Adeniji ya kara da cewa, a kwanan baya, mambobin kwamitin zartaswa na Kawancen Kasashen Afirka sun riga sun sami ra'ayi daya kan matsayin da kasashen Afirka za su dauka a kan yin gyare-gyaren kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, wato sun bukaci majalisar da ta bayar da a kalla kujerun din din din guda 2 na kwamitin sulhu ga kasashen Afirka. Kasarsa za ta yi kokarin neman samun daya daga cikin wadannan kujeru 2, bisa shirin da abin ya shafa da Kawancen Kasashen Afirka ya gabatar.(Tasallah)
|