Wata kungiyar shari'a ta Kawancen Kasashen Afirka wadda ke karkashin shugabancin ministan tsaron kasar Afirka ta Kudu Mosiuoa Lekota ta sauka kasar Cote d'Ivoire a ran 13 ga wannan wata don ba da taimako wajen maido da aikin yunkurin shimfida zaman lafiya a kasar.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, wannan kungiya tana kunshe da kwararrun shari'a daga kasashen Afirka ta Kudu da Burundi da kuma Rwanda. Za su gana da wakilan dukan rukunonin siyasa na kasar daya bayan daya, za su kuma gabatar da shawarwari ga gwamnatin kasar kan yin gyare-gyaren shari'a don tabbatar da sharuddan 'yarjejeniyar zaman lafiya ta Marcoussis' da rukunonin kasar suka rattaba hannu tare, ta yadda za a iya maido da aikin yunkurin shimfida zaman lafiya a kasar.(Tasallah)
|