Ran 10 ga wata, dakarun ' the New Forces' wato Sabuwar Runduna wadanda ba sa ga maciji da gwamnatin kasar Kodivwa a da sun bayar da wata sanarwa, inda suka shelanta cewa, suna tsayawa kan bakarsu domin matakan soja da sojojin gwamnati ka iya dauka.
Cikin sanarwar, an ce, dauki ba dadi da aka yi a cikin yankin da ba na soja ba da ke yammacin kasar a kwanakin baya ka iya haifar da yake-yake. An yi gargadin cewa, idan an kai hari ga dakarun sabuwar runduna, to, ba za su tsaya kan daukan matakan kare kai kawai ba. (bello)
|