Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-03-11 10:46:15    
Kotun koli ta Namibia ta neme a sake kirga kuri'un da aka kada wajen zaben majalisar dokoki

cri
A ran 10 ga wata, kotun koli ta kasar Namibia ta yanke hukunci, inda ta nemi kwamitin zabe na kasar da ya sake kirga kuri'un da aka kada a bara na zaben majalisar dokokin kasar. Amma kuma, kotun ta ki yin shelar soke sakamakon zaben.

Alkalin kotun koli ya nemi a fara aikin sake kirga kuri'u tun daga ran 13 ga wannan wata, kuma ya kamata a gama shi kafin ran 20.

A gun zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki da aka gudanar da shi a ran 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba da ya shige a kasar Namibia, kungiyar jama'ar kudu maso yammacin Afirka wadda ke kan karagar mulkin kasar tare da dan takararsa Hifikepunye Pohamba sun ci zaben bisa yawan kuri'un da suka samu na fiye da 75%. Amma daga bisani, jam'iyyun adawa guda biyu na kasar sun nemi kotun koli da ta soke sakamakon zaben bisa dalilin da suka bayar cewa akwai matsala a cikin kirgen wadannan kuri'u.(Lubabatu Lei)