A ran 10 ga wata, kwamitin kawancen kasashen Turai ya bayar da sanarwar labarai cewa, kwamitin kawancen kasashen Turai ya riga ya amince da ma'aikatar ba da taimakon jin kai da ke karkashin jagorancinsa da ta bai wa kasar Zimbabuwe taimakon jin kai da yawansa ya kai Euro miliyan 15 da kuma kasar Colombia wadda ita ma za a ba ta taimakon nan da yawansa ya kai Euro miliyan 12.
An ce, za a bai wa kasashen nan biyu wannan taimakon jin kai ne a fannonin abinci da ruwan sha da kuma kayayyakin kiwon lafiya. Ban da wannan, za a ba wa Zimbabuwe taimako a fannin farfado da ayyukan noma. A bangaren Colombia kuma, za a bayar da agajin gaggawa ga 'yan gudun hijira nata da ke kasashen Ecuador da Venezuela.(Lubabatu Lei)
|