Kwanakin baya, an yi dauki ba dadi a birnin Hobyo da ke tsakiyar kasar Somali. Zuwa ran 7 ga wata, mutane a kalla 16 sun rasa rayukansu sabo da arangamar da aka yi.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, dauki ba dadin ya barke a tsakanin dakarun rukunoni 2 na kabilar Hawiye a ran 5 ga wata. Wadannan dakaru su kan fafata rikici a tsakanin juna a cikin watannin baya. A makon da ya gabata, lokacin da Abdullahi Yusufu, shugaban wucin gadi na kasar ke ziyara a yankin, ya yi kokari domin neman shawo kan bangarorin 2 da su rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta. (Bello)
|