Kwanan nan, wasu kasashe da kungiyoyin duniya sun mayar da martani a kan kudurin da kasar Syria ta furta a ran 5 ga wata game da janye sojojinta daga Lebanon mataki bisa mataki.
A ran 6 ga wata, mai ba da shawara ga fadar mulkin Amurka ta "White House", Dan Bartlett ya bayyana cewa, Amurka da kasashe masu abuta da ita za su ci gaba da matsa wa Syria lamba, don nemanta da ta janye dukannin sojojinta daga Lebanon nan da nan.
A sa'i daya kuma, a ran 5 ga wata, babban sakataren gamayyar kasashen Larabawa Amr Moussa ya bayar da wata sanarwa, inda ya nuna babban yabo ga kudurin da Syria ta tsai da game da janye sojojinta, kuma yana ganin cewa, wannan mataki ne mai kyau da ta dauka wajen aiwatar da "yarjejeniyar Taif" da kiyaye huldar da ke tsakanin Syria da Lebanon, wanda kuma ya dace da kuduri mai lambar 1559 na kwamitin sulhu na MDD.
Ban da wannan, a ran 5 ga wata, ministan harkokin waje na Masar Ahmed Abu Gheit ya bayyana cewa, wannan aikin da Syria ta yi zai tabbatar da kwanciyar hankali a Lebanon da kuma tsaro a Syria a karshe.(Lubabatu Lei)
|