Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-03-07 08:54:38    
Za a yi matsuguni wa sojojin Syria da ke Lebanon zuwa Bekaa Valley

cri
A ran 6 ga wata, ministan tsaron kasar Lebanon Abdel Rahim Mrad ya fadi a birnin Beirut cewa, bayan shugabannin Lebanon da Syria sun yi shawarwari a ran 7 ga wata, a kai a kai ne za a gusar da sojojin Syria zuwa yankin Bekaa Valley da ke gabashin kasar Lebanon.

A ran 5 ga wata, shugaba Emile Lahoud na kasar Syria ya shelanta cewa, daga farko za a gusar da sojojin Syria da ke zaune a kasar Lebanon zuwa yankin Bekaa Valley, daga baya, za a tsugunar da su a yankin dake kusa da iyakar kasashen biyu.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, a ran 7 ga wata, shugaba Bashar da takwaransa na kasar Lebanon Mr. Lahoud za su yi shawarwari, inda za su tattauna kan tsara tsarin janye jikin sojojin Syria kuma da karshen lokacin janye jikinsu daga kasar Lebanon.

Bisa labari daban da aka bayar, an ce, a ran 6 ga wata, shugaba Lahoud na kasar Lebanon ya shelanta cewa, tun daga ran 9 ga wata ne za a yi shawarwari kan yadda za a kafa sabuwar gwamnatin kasar a gun majalisar dokokin kasar. (Sanusi Chen)