A ran 5 a wannan wata, bayan da shugaban kasar Syria Bashar Al Assad ya yi shelar janyewar sojoji bisa mataki mataki, sai bangarori daban daban sun yi martani a wannan rana bi da bi.
A wannan rana, shugaban kasar Lebanon Emile Lahoud ya bayar da sanarw cewa, jama'ar Lebanon ba za su manta da sadaukar da rai da bangaren Syria ya yi domin kasar Lebanon ba. Amma rukunonin 'yan hamayya na kasar Lebanon sun yi martani iri daban daban a kan shirin janyewar sojojin Syria.
Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Amurka ta bayyana cewa, bayanin da Bashar ya yi a wannan rana bai ishe ba, dole ne kasar Syria ta janye sojojinta kwata kwata. Sanarwar ma'aikatar harkokin waje ta kasar Faransa ta bayyana cewa, kasar Faransa ta yi fatan kasar Syria ta janye sojojinta kwata kwata kuma nan da nan daga kasar Lebanon.
Kasashen Larabawa sun yi martani mai yakini ga bayanin da Bashar ya yi a wannan rana. Masar ta yi maraba da shirin janyewar sojojin Syria.Ministan harkokin waje na kasar Jordan ya bayyana cewa, kasar Jordan ya karfafa kan muhimmancin da bangaren Syriya ke aiwatar da kuduri mai lamba 1559, sa'anan kuma Qatar ita ma ta bayar da sanarwa don nuna maraba da shirin nan.(Halima)
|