Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-03-04 18:41:12    
Cote dI'voire tana maraba da kudurin da majalisar dokokin EU ta yi game da halin da ake ciki a kasar

cri
A ran 3 ga wata, kakakin fadar shugaban kasar Cote dI'voire ya bayar wata sanarwa a birnin Abidjan na kasar cewa, shugaba Laurent Gbagbo yana maraba da kudurin da aka zartas kwanan baya a gun taron majalisar dokokin kawancen kasashen Turai game da halin da ake ciki a kasar. Shugaba Gbagbo yana ganin cewa, wannan kuduri zai ba da amfani wajen farfado da zaman lafiya a kasarsa.

Wannan sanarwa ta ce, kudurin ta nemi membobin kawancen kasashen Turai da su nuna cikakken girmamawa ga ainihin iko na jama'ar kasar Cote dI'voire bayan da bangarori daban-dabam na Cote dI'voire suka kulla yarjejeniyar Marcous da yarjejeniyar Accra kan maganganun watsi da makaman bangarori daban-daban da jefa kuri'ar raba gardama kuma da kiran babban zabe cikin 'yanci. Saboda haka, shugaba da jama'ar kasra Cote dI'voire suna maraba da wannan kuduri domin suna ganin cewa, wannan babbar gudummawa ce da majalisar dokokin kawancen kasashen Turai ta bayar wa ayyukan shimfida zaman lafiya a kasar ta hanyar kafa doka. (Sanusi Chen)