Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-03-04 11:34:26    
Kasashen Cyprus da Afika ta Kudu sun yi suka kan rahoton hakkin dan Adam na kasar Amurka

cri
Gwamnatin kasar Cyprus ta kai suka kan ma'aikatar harkokin waje ta kasar Amurka a ran 3 ga wannan wata saboda bayani maras kan gado da ya shafi kasar Cyprus cikin rahoton da ta bayar a kan hakkin dan Adam a kwanan nan. Ban da wannan kuma, a ran 2 ga wannan wata, gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ita ma ta musunta zargin da kasar Amurka ta yi mata cikin rahotonta kan halin da take ciki a fannin hakkin dan Adam.

Majalisar dokokin kasar Cyprus ta zartas da wani kudirin musamman a ran nan cewa, ko kusa gwamnatin kasar ba ta amince da rahoton da kasar Amurka ta bayar ba. Ma'aikatar harkokin waje ta kasar ita ma ta kirawo mukadashin babban wakilin kasar Amurka da ke kasar, inda ta kai suka mai tsanani, tana ganin cewa, duk wadannan zargi ba su da kan gado, kuma sun kawo wa mulkin kan kasar illa.

A ran 2 ga watan nan, kakakin gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ya bayyana cewa, kiri da muzu, ma'aikatar harkokin waje ta kasar Amurka ta yi mata sharhi kan halin da take ciki a fannin hakkin dan Adam, ba tare da fahimtar al'adunta sosai ba, Amurka tana ganin cewa, yana kasancewa da babbar matsalar hakkin dan Adam a cikin kasar Afirka ta Kudu, wannan wani irin danyen aiki.(Tasallah)