Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-03-02 20:08:02    
Sojojin M.D.D. da ke Kongo Kinshasa sun kashe dakaru fiye da 50

cri

A ran 2 ga wata, wani jimi'in kungiyar musamman da M.D.D. ta aika zuwa Kongo Kinshasa ya fayyace cewa, a ran 1 ga wata a wani wurin da ke da nisan kilomita 30 a tsakaninsa da Bunia, wani muhimmin birnin jihar Ituri, sojojin kiyaye zaman lafiya na M.D.D. sun yi arangama da dakaru 'yan kabilu na wurin, kuma sun kashe dakaru fiye da 50 a cikin yakin.

Domin neman masu laifi wadanda suka yi kisan gilla ga sojojin kiyaye zaman lafiya guda 9 na kasar Bangladech. a makon jiya, a ran 1 ga wata sojojin kiyaye zaman lafiya sun damke sojoji fararen hula a wurin da ke kusa da jihar, kuma sun yi arangama da juna, inda suka kashe dakaru fiye da 50.

Ban da wannna kuma, kakakin kungiyar musamman ta M.D.D. da ke Kongo Kinshasa ya fayyace cewa, an riga an kama shugaban sojoji fararen hula na kabilun kasar wanda ake yi tuhumarsa da laifin kai farmaki kan sojojin kiyaye zaman lafiya na M.D.D.

A ran 25 ga watan Fabrairu, sojojin kiyaye zaman lafiye 20 na Bangladech sun shiga tarko da aka dana musu a jihar Ituri, wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojoji 9, yayin da mutane 11 suka ji rauni. (Umaru)