A ran 1 ga wata da yamma, wakilin musamman na babban sakataren MDD da ke kasar Kongo(Kinshasa) ya bayyana cewa, an riga an kama shugaban sojojin kabila na kasar Kongo(Kinshasa) wanda ake tuhumarsa da laifin kai farmaki ga sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD.
Bisa labarin da muka samu daga tawagar musamman ta MDD da ke kasar Kongo(Kinshasa), an ce, bi da bi ne gwamnatin kasar Kongo(Kinshasa) da sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD suka dauki matakan cafke shi a shiyyoyin Kinshasa da Ituri, sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD sun gamu da dagiya daga dakarun kabilar wurin. Amma tawagar musamman ta MDD da gwamnatin kasar Kongo(Kinshasa) ba su fayyace yawan wadanda aka kama su da asalinsu ba.(Danladi)
|