A ran 28 ga watan Fabrairu, kungiyoyi masu rike da makamai kuma masu adawa da gwamnati sun shelanta cewa, domin a wannan rana, dakarun gwamnati sun kai farmaki kan sansaninsu da ke yammacin kasar a wannan rana da sassafe, masu rike da makamai na wadannan kungiyoyi dukkansu sun fara shiga cikin halin shirin yaki.
Wata sanarwar da kungiyoyi masu rike da makamai kuma masu adawa da gwamnati suka bayar ta ce, farmakin da aka yi "matakin shirin yaki ne", "ya kuma binne dukkan kokarin da kawancen kasashen Afirka da kasashen duniya suka yi wajen sulhunta rikicin Cote dI'voire".
A wannan rana da maraice, dakarun gwamnatin ma sun bayar da wata sanarwar cewa, suna mai da hankali sosai kan wannan, kuma suna daukar dukkan wajababbun matakai domin sarrafa halin da ake ciki. (Sanusi Chen)
|