Bisa labarin da aka samu an ce, a halin yanzu yawan man fetur da aka gano a Afrika ya zarce ganguna biliyan 98.
Wannan labari ya ce, da ya ke kasashe da yawa suna safiyon man fetur, yawan man fetur da za a gano zai karu. Ya zuwa shekara ta 2020, yawan man fetur da za a murdo a Afrika zai karu da kashi 68 cikin kashi 100.
A shekara ta 2004, muhimman kasashen Afrika da suka fitar da man fetur su ne Nigeria, da Libia da Algeria da angola da Masar da Sudan da sauransu. (Dogonyaro)
|