A ran 25 ga wannan wata, a nan birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, wakiliyar majalisar gudanarwa ta kasar madam Chen Zhili ta gana da kungiyar wakilan al'adu ta kasar Tanzania wadda ke yin ziyara a nan.
A lokacin ganawar da ta yi, madam Chen ta bayyana cewa, gwamnatoci da jama'ar kasashen nan 2 suna da abokantaka ta gargajiya da ingantacciyar huldar hadin gwiwa da sada zumunci a tsakaninsu. Dukan shugabannin kasashen nan 2 na da da na yanzu sun dora muhimmanci sosai kan dangantakar da ke tsakanin kasashen nan 2, bayan da aka kafa huldar diplomasiyya a tsakaninsu, kasashen Sin da Tanzania sun yi ta yin mu'amala da hadin gwiwa a fannonin al'adu da aikin ba da ilmi, a sakamakon haka, sun kara fahimtar juna da zurfafa zumuncin da ke tsakaninsu.(Tasallah)
|