Ran 24 ga wata, wani jami'in kasar Nijeriya ya tabbtar da cewa, cikin makonni 2 da suka wuce, cutar kwalara da ke brbazuwa a jihar Oyo ta kudu maso yammacin kasar Nijeriya ta yi sanadiyyar mutuwa a kalla mutane 46.
Bisa labarin da jimi'in nan ya bayar, an ce, wurin da aka samu bazuwar annoba shi ne yankin Kusa da ke dab da birnin Ibadan, fadar gwamnatin jihar Oyo, kuma yawancin mazaunan masu haka ma'adinan da ke karkashin kasa ne. Bisa binciken da aka yi, an ce, dalilin da ya haifar da annoba shi ne gurbacewar ruwan sha. Yanzu ban da mutane 46 wadanda suka riga mu gidan gaskiya, akwai wasu fiye da 100 suna cikin asibiti sabo da cutar. (Bello)
|