Ran 24 ga wata, a birnin Athens, fadar mulkin kasar Girika, Constis Stephanopoulos, shugaban kasar ya gana da shugaba Mbeki na kasar Afirka ta Kudu wanda ke ziyara a kasar Girika, inda bangarorin 2 suka yi kira tare ga kawancen kasashen Turai da ya kara ba da kudin agaji domin bunkasa kasashen Afrika.
A gun hadadden taron maneman labarai da suka yi a bayan ganawarsu, shugabannin 2 sun nuna cewa, ya kamata a kara hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen arewacin duniya da wadanda ke kudancin duniya. Kuma kungiyar EU ita ke da alhaki a wuyanta wajen ba da taimako ga kasashen Afrika wajen bunkasa tatatlin arziki, domin sai dai an samu bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afirka ne, za a iya shawo kan kwararar 'yan gudun hijara daga Afirka zuwa cikin kasashen Turai. (Bello)
|