|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2005-02-24 17:02:18
|
Majalisar togo ta kirayi gamayyar kasa da kasa da su fahimci halin da Togo ke ciki yadda ya kamata
cri
Labari daga Kamfanin Dillancin Labaru na Xinhua ya bayyana cewa, a ran 23 ga wannan wata a birnin Lome, hedkwatar kasar Togo, majalisar kasar ta kira taron musamman na 5, inda ta kirayi gamayyar kasa da kasa da su fahimci halin siyasa da kasar Togo ke ciki yadda ya kamata.
Taron ya kirayi dukkan kasashe masu kishin zaman lafiya da adalci da su dauki ra'ayi yadda ya kamata a lokacin da suke binciken halin yanzu da kasar ke ciki. Taron yana ganin cewa, matakin da majalisar Togo ta dauka na gyara tsarin mulkin kasa da kuma zabar Mr Faure Gnassingbe don ya zama shugaban majalisar yana dacewa, ko kadan bai yi daidai da abin da wasu mutanen da ke da mugun nufi suka bayyana ba da cewar wai juyin mulki ne aka yi .(Halima)
|
|
|