Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-02-24 11:08:03    
Kenya tana son kara hadin gwiwar kiyaye muhalli tare da kasar Sin

cri
A ran 23 ga wata, ministan muhalli da albarkatun kasa na Kenya Kalnozo Musyoka ya bayyana cewa, Kenya ta nuna yabo kan kokarin da gwamnatin kasar Sin take yi shekara da shekaru wajen kiyaye muhallin gida da kuma hadin gwiwar kiyaye muhallin duniya, kuma tana son kara hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannin kiyaye muhallin dan Adam.

Mr.Musyoka ya ce, shawarar da kasar ta bayar da gun taron hadin gwiwar kiyaye muhalli tsakanin Sin da Afirka shawara ce mai kyau, kuma ya kamata a nuna yabo kan goyon bayan da kasar Sin ta bai wa kasashen Afirka a fannin kiyaye muhalli. Ya ci gaba da cewa, yanzu, an riga an daddale yarjejeniyoyi da kuma takardun kara fahimtar juna tsakanin Sin da Kenya a fannonin fasahohin tattalin arziki da makamashi da albarkatun kasa, yana fatan a nan gaba, kasashen nan biyu za su kulla yarjejeniyar hadin gwiwa a fannin kiyaye muhalli. (Lubabatu Lei)