Ran 23 ga wata Wani sansanin ajiye albarusai da ke kudancin kasar Sudan ya fashe, mutane 20 ne suka mutu kuma fiye 50 suka ji rauni.
Yan sanda sun ce, al'amarin ya faru ne a karfe 12 da minti 30, kuma ya shafa lokacin fiye da awa daya. Kuma wata kasuwa da wasu unguwannin jama'a sun kama wuta.
Yanzu sojojin Sudan sun riga sun rufe wurin, suna watsa mutanen da ke wurin kuma aika da masu jin rauni zuwa asibiti. Ya zuwa maraice, an riga an kashe wuta.
|