A ran 23 ga wannan wata da dare, mataimakin firayin ministan kasar Sin Zeng Peiyan ya bayar da wani jawabi lokacin da ya isa birnin Brazzaville, inda ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan za a yalwata huldar aminci da hadin gwiwa ta gargajiya tsakaninta da kasar Congo Brazzaville.
Mr.Zeng ya ce, tun bayan da aka kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen nan biyu, dangantakar da ke tsakaninsu tana bunkasa lami lafiya. Makasudin wannan ziyarar da yake yi shi ne karfafa dankon zumunci da fahimtar juna da kuma samun sabbin hanyoyin hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki tsakanin bangarorin biyu. Mr.Zeng ya kara da cewa, kasar Sin tana son karfafa hadin gwiwa tsakaninta da kasar Congo Brazzaville a fannonin noma da masana'antu da makamashi da dai sauransu.(Lubabatu Lei)
|