|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2005-02-23 14:59:23
|
Ya kamata a yi kokarin samun kujeru 2 na zaunannun wakilan kwamitin sulhu ga kasashen Afirka
cri
A ran 22 ga wata, an gama taron ministocin harkokin waje na kasashe 15 na Afirka wanda aka shafe kwanaki 3 ana yin sa a birnin Mbabane, hedkwatar kasar Swaziland, a gun taron wadannan ministocin harkokin waje gaba dayansu sun yarda da cewa za a ba da shawara ga kawancen kasashen Afirka domin samun kujeru 2 na zaunannun wakilan kwamitin sulhu ga kasashen Afirka cikin gyare-gyaren tsarin hukumomin M.D.D. da za a yi a nan gaba, ta yadda Afirka za ta kara ba da babban taimako ga harkokin duniya baki daya.
Sabo da kawancen kasashen Afirka bai kai da samun ra'ayi daya kan wannan batu a watan jiya ba, shi ya sa a danka wa ministocin harkokin waje na kasashe 15 ciki har da Nijeriya da Angola da Botswana da Aljeriya da su yi taro don tattauna wannan matsala da ba da shawara a kai. (Umaru)
|
|
|