Ran 21 ga wata, 'yan sanda 300 na kasar Jamhuriyar Dimokuradiyya ta Kongo sun fara aikinsu a birnin Bunia, fadar gwamnatin yankin Ituri da ke arewa maso gabashin kasar. Wannan karo na farko ne da gwmnatin kasar ta girke 'yan sanda a yankin bayan shekaru 8 da suka wuce.
A daidai wannan rana, Theophile Mbemba, ministan kasar mai kula da harkokin gida ya ba da jawabi, inda ya yi kira ga jama'a da masu mukami da ke yankin da su yi kokari domin wanzar da sulhuntawa da zaman lafiya a tsakanin kabili dabam daban. Ya ce, kamata ya yi, mutane miliyan 6 da ke zaune a yankin Ituri wanda fadinsa ya kai muraba'in kilomita dubu 65, su yi zamansu cikin lumana, kuma su yi amfani da albarkacin kasar da Allah ya fuwace yankin domin raya kansu. (Bello)
|