Ran 21 ga wata, kasar Nijeriya ta yi "taron kyautata harkokin siyasa na duk kasa" a babban birninta Abuja, kuma ta fara kayutata tsarin mulkinta na yanzu.
Bisa bayanin da wani jami'in Nijeriya ya yi, Shugaban kasar da wakilai fiye da 400 na jihohin kasar daban daban sun halarci bikin. A cikin taron da za a shafe watanni uku, masu halartar taron za su gabatar da matakai masu amfani don kyautata tsarin mulki na yanzu. Ban da haka kuma, za su tattauna kan yaya za a iya daidaita huldar da ke tsakanin kubilu daban daban na kasar, da kara ba su damar fadin albarkacin bakinsu kan harkokin siyasar kasa da zaman rayuwa da kuma huldar dake tsakanin gwamnatin tarayyar kasar da gwamnatocin jihohi.
|