|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2005-02-21 17:26:23
|
 |
Kasar Sin da kasar Afirka ta Kudu za su kira taron tattaunawa kan hadin guiwa a ma'aikatar haka ma'adinai
cri
Hadaddiyar kungiyoyin ma'aikatar haka ma'adinai ta kasar Sin da kungiyar kasuwanci ta ma'aikatar haka ma'adinai ta kasar Afirka ta Kudu za su kira taro na farko na fadin albarkacin bakinka kan ma'aikatar haka ma'adinai a birnin Johannesburg, cibiyar tattalin arziki ta kasar Afirka ta Kudu tun daga ran 9 zuwa ran 11 ga watan Mayu na shekarar nan. Wannan zai samar da wata muhimmiyar damar kara yin hadin guiwa da zuba jari a ma'aikatar haka ma'adinai a tsakanin kasashen nan biyu.
Ofishin hadaddiyar kungiyoyin ma'aikatar haka ma'adinai ta kasar Sin da ke kudancin Afirka da ke shirya wannan taro ya bayyana cewa, za a gayyaci wakilai fiye da dari 2 na kamfanonin haka da binciken ma'adinai da hukumomin nazari kan ma'aikatar haka ma'adinai da kamfanonin ciniki da kayan ma'adinai na kasashen nan biyu da su halarci taron, inda za su yi musaya da tattaunawa kan yiyuwar kara yin hadin guiwa a tsakanin kasar Sin da kasar Afirka ta Kudu har da tsakanin kasar Sin da sauran kasashen Afirka a ma'aikatar haka ma'adinai. (Sanusi Chen)
|
|
|