A ran 20 ga wata da dare, agogon wurin, mataimakin firayin ministan kasar Sin Zeng Peiyan ya isa birnin Nairobi, babban birnin kasar Kenya, don yin ziyara ta kwanaki 3 a kasar.
A cikin takardar jawabin da Mr.Zeng ya bayar a filin jirgin sama, ya ce, wannan ziyarar da yake yi zai kara fahimtar juna da dankon zumunci da kuma hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu.
An ce, a lokacin ziyarar, Zeng Peiyan zai yi shawarwari tare da mataimakin shugaba da kuma shugaban kasar bi da bi, kuma zai halarci taron wakilai na 23 na hukumar kyautata muhalli ta MDD da kuma bikin bude dandalin tattaunawar muhalli na ministocin kasa da kasa, haka kuma zai halarci taron hadin gwiwar muhalli tsakanin Sin da Afirka na karo na farko.(Lubabatu Lei)
|