Shugaban kawancen kasashen Afirka kuma shugaban kasar Nijeriya Olusegun Obasanjo ya gana da kungiyar wakilan gwamnatin kasar Togo wadda shugaban kasar Faure Gnassingbe yake shugabanta a birnin Abuja, babbar fadar kasar Nijeriya a ran 17 ga watan nan, inda bangarorin biyu suka yi musanyar ra'ayoyinsu kan halin da kasar Togo take ciki yanzu.
Bisa labarin da muka samu daga wani jami'in Nijeriya wanda ya halarci shawararin, an ce, Mr. Obasanjo ya sake nuna wa Mr. Faure fatansa cewa, yana so a maido da odar tsarin mulkin kasar Togo da kuma yi babban zaben shugaban kasar tun da wuri.
Kuma wani jami'in kungiyar wakilan kasar Togo ya ce, bangaren Togo ya riga ya ji shawarar da shugaba Obasanjo ya gabatar, kuma zai yi nazari a kan wannan. Haka kuma jami'an kungiyar ECOWAS sun halarci shawarwarin da aka yi a ran nan.(Kande Gao)
|