Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-02-17 20:40:31    
An sami fashewar bom a hedkwatar kasar Somaliya

cri
A ran 17 ga wata a birnin Mogadishu, hedkwatar kasar Somali, an sami wata fashewar bom wadda ta yi sanadiyar mutawar a kalla mutane 2, yayin da mutane 6 suka ji rauni.

A wannan rana, wani babban jami'i na Somali wanda ba ya son a fadi sunansa ya ce, an sami wannan fashewa ne sabo da bom da aka ajiye cikin wani babur da ke bakin kofar ma'aikatar harkokin waje ta Somali. Mutane 2 da suka mutu dukkansu mutanen somali ne, daga cikin mutane 6 da suka ji rauni kuwa da akwai mutane 3 wadanda suka ji rauni mai tsanani.

Wannan jami'i ya kuma bayyana cewa, sabo da jerin gwanon motoci na karamar kungiyar yin bincike ta kawancen kasashen Afirka wadda ke yin binciken halin kwanciyar hankali a birnin Mogadishu zai bi ta wannan wuri, shi ya sa mai yiwuwa ne masu tsattsauran ra'ayi na Somali suka haddasa wannan fashewar bom domin yin adawa da kawancen kasashen Afirka da ya jibge sojojin tsaro a kasar. Ban da wannan kuma wannan hargitsin ya bayyana cewa, har ila yau ba a samu kwanciyar hankali a birnin Mogadishu ba tukuna, sabo da haka gwamnatin rikon kwarya ta somali da ke birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya za ta dakatar da lokacin komarta kasar. (Umaru)