Bisa labarin da aka bayar a ran 16 ga watan nan an ce, kotun Koli ta kasar Swiss ta yanke hukuncin karshe cewa, kasar Swiss za ta mayar wa gwamnatin Nigeria da dollar miliyan 500 da tsohon shugaba Abacha ya ajiye a kasar Swiss.
Daga watan Nowamba na shekara ta 1993 ne Sani Abacha ya hau kan karagar mulki, a watan Yuni na shekara ta 1998 ne ya mutu sabo da ciwon zuciya. Gwamnatin Nigeria ta zargi Abacha sabo da ya kwashe kudin kasar Nigeria har dollar biliyan 2.2, kuma ya boye kudin nan a bankunan kasashen waje. Daga shekara ta 1999 ma'aikatar shari'a ta Swiss ta amince da rokon shari'a na Nigeria, ta daskare kudin da Abacha ya ajiye a bankunan Swiss har dollar miliyan 700. (Dogonyaro)
|