Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-02-04 16:29:45    
Gwamnatin Uganda ta sake dakatar da wutar yaki a tsakaninta da dakaru masu adawa da ita

cri
Bisa umurnin da shugaba Yoweri Kaguta Museveni ya bayar, gwamnatin kasr Uganda ta sake dakatar da bude wutar yaki a tsakaninta da dakarun sa kai masu adawa da ita a yankin dake arewacin kasar tun daga karfe 7 na ran 4 ga watan nan, agogon wurin har na tsawon kwanaki 18 masu zuwa. Dalilin da ya sa gwamnatin Uganda ta yi haka shi ne "Dakarun 'Yan tawaye na Lord Resistence" wadanda suke adawa da gwamnatin za su iya farfado da yin shawarwarin neman zaman lafiya har za a iya kulla wata yarjejeniyar kawo karshen bude wutar yaki a tsakaninsu da gwamnatin.

Jaridar gwamnati da ake kiranta New Vision ta kasar da aka wallafa ta a wannan rana ta tabbatar da wannan labari. Tuhakana Rugunda, ministan harkokin gida na kasar Uganda wanda ke shugabantar rukunin shawarwarin, ya ce, gwamnatin ta yarda da sake dakatar da bude wutar yaki ya bayyana cewa, gwamnatin ta nuna goyon baya ga yunkurin kawo karshen rikicin da ke kasancewa a arewacin kasar cikin lumana. Mr. Rugunda ya kuma yi fatan dakarun sa kai masu adawa da gwamnatin za su iya sa hannu a kan yarjejeniyar kawo karshen wutar yaki domin sa ayar rikicin da ya shafe shekaru 18 ana yinsa a arewancin kasar. (Sanusi Chen)