A ran 3 ga wata, bankin raya Afirka ya bayyana cewa, zai bayar da kudin taimako da yawansa ya kai dollar Amurka miliyan 18 da dubu 600 ga kasar Saliyo, don farfado da ayyukan noma da aka lallata lokacin yakin basasa da aka shafe sekara da shekaru ana yi a kasar.
A cikin wata sanarwar da banki ya bayar a ran nan, an ce, za a yi amfani da kudin nan ne wajen mayar da ayyukan noma da manoma na kasar suka daina sabo da yaki, da kuma gyara kayayyakin noma da aka bata.
Bisa kidayar da aka yi, an ce, kudin nan zai amfana wa manoma kimanin dubu 140 daga iyalai sama da dubu 20 na kasar.(Lubabatu Lei)
|