A ran 3 ga wata, a birnin London, tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela wanda ke yin ziyara a kasar Ingila, ya yi kira ga kasashe masu wadata da su ba da taimako ga kasashe masu talauci don kubutar da su daga mawuyacin hali.
Mr.Mandela ya yi kira ne a gun wani biki mai suna "mayar da talauci don ya zamo tarihi" da aka shirya a London. hakan nan kuma yana fatan kasashe masu sukuni za su dauki matakai tun da wuri, ta yadda za a kubutar da matalauta miliyoyi na duk duniya daga talauci.
A ran 4 ga wata kuma,, Mr.Mandela zai halarci taron ministocin kudi na kasashen yamma 7 da za a yi a London, inda kuma zai bayar da jawabi, don yin kira ga ministocin kudi na kasashe masu sukuni da su kara ba da taimako ga kasashe masu tasowa wajen daidaita matsalar talauci.(Lubabatu Lei)
|