Babban sakataren M.D.D. Kofi Annan ya gabatar da wani rahoto ga kwamitin sulhu na M.D.D. a ran 3 ga watan nan, inda ya ba da shawara ga kwamitin sulhu da ya amince da aikawa da sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa kudancin kasar Sudan tun da wuri.
Haka kuma Mr. Annan ya ce, dole ne a dauki matakai nan da nan don sa kaimi ga gwamnatin Sudan da dakaru masu yin adawa da gwamnatin da ke kudancin kasar da su aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da aka daddale tsakaninsu, sabo da haka, ya kamata a aika da rundunar sojojin M.D.D. na kiyaye zaman lafiya da ke hade da sojoji fiye da dubu goma da kuma 'yan sanda fiye da 750 zuwa shiyyar kudancin kasar Sudan.
A sa'i daya kuma, Mr. Annan ya jaddada cewa, taimakon da kasashen duniya suke bayarwa yana da matukar muhimmanci ga sake gina kasar Sudan. Ban da wannan kuma ya nuna cewa, samun zaman karko a shiyyar kudancin kasar Sudan zai bayar da taimako ga warware matsalar Darfur tun da wuri.(Kande Gao)
|