|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2005-02-03 11:31:52
|
Wasu tsofaffin dakarun kasar Liberia sun koma makaranta
cri
Wani jami'in kungiyar musamman ta kiyaye zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya ta tura zuwa kasar Liberia ya tabbatar a ran 2 ga wannan wata cewa, ya zuwa yanzu kungiyar musamman ta riga ta tattara issashen kudi don tabbatar da komawar tsofaffin dakaru kimanin dubu 4 na kasar cikin makaranta, wadanda suka bar makaranta a sabili da rashin kudi.
Wannan jami'i ya kara da cewa, kafin mako mai zuwa, wannan kungiya ta musamman za ta kammala wannan aiki tare da makarantun wurin don tabbatar da komawar wadannan tsofaffin dakaru makaranta tun da wuri.(Tasallah)
|
|
|