A ran 2 ga wannan wata, gwamnatin kasar Cote d'Ivoire ta yi maraba da kudurin da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya tsai da a ran 1 ga wannan wata kan kara karfin garkama mata takunkumin makamai.
A ran nan ministan kula da sulhuntawar al'ummar kasar Sebastien Djedje Dano ya bayyana cewa, idan wannan kuduri zai iya ba da taimako wajen sa aya ga rikicin da kasar ke fuskanta a yanzu, to, gwamnatin kasar za ta yi maraba da shi, amma idan wannan kuduri ya kayyade gwamnatin kasar kawai, to, ba zai ba da taimako wajen yunkurin shimfida zaman lafiya a kasar ba. A sa'i daya kuma Mr. Dano ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su aiwatar da wannan kuduri a tsanaki, kuma su dauki tsattsauran matakai don hana shigar da makamai cikin yankin kasar na arewa da ke hannun tsohon dakarun adawa da gwamnatin kasar.(Tasallah)
|