Ran 2 ga watan nan, bisa shugabantar Muse Sudi Yalahow, dan majalisar kasar Somali ta wucin gadi, kuma ministan kasuwancin kasar mai rikon kwarya, 'yan majalisar kasar 30 sun koma birnin Mogadishu, fadar mulkin kasar Somali, wannan yana alamantar cewa, gwamnati da majalisa ta kasar Somali sun fara komawa gida domin aikinsu.
A gun filin saukar jiragen sama na birnin Mogadishu, 'yan majalisar sun gamu da jama'a fiye da 600, wadanda suka taru a wurin domin nuna musu marhabin. Mista Yalahow ya nuna cewa, za a kaurar da majalisa da gwamnati na kasar cikin gida sannu a hankali.
Bisa labarin da muka samu, wadannan 'yan majalisa za su yi ziyara a yankin tsakiyar kasar Somali. (Bello)
|