Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-02-03 10:27:35    
Mr. Chirac ya fara ziyararsa a kasar Senegal

cri

Shugaban kasar Faransa Jacques Chirac ya sauka birnin Dakar, hedkwatar kasar Senegal a ran 2 ga wannan wata don ziyara ta yini 3.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, lokacin ziyararsa a kasar, Mr. Chirac zai yi shawarwari da shugaban kasar Abdoulaye Wade kan kara karfin hadin gwiwa tsakanin kasashen nan 2 da halin da yankin yammacin Afirka ke ciki da kuma batun ba da taimakon kudi da gamayyar kasa da kasa ta yi don ba da taimako wajen bunkasuwar zamantakewar al'umma da tattalin arziki na matalautan kasashe. Ban da wannan kuma, Mr. Chirac zai halarci wani karamin taron koli kan ingiza bunkasuwar aikin noma na wurin tare da sauran shugabanni 5 na kasashen yammacin Afirka.(Tasallah)