Ran 2 ga watan nan, a birnin Maputo, fadar mulkin kasar Mozambique, Armando Guebuza, sabon shugaban kasar, ya yi rantsuwar kama mulki, yadda ya zama mutumi na uku wanda ya zama shugaban kasar Mozambique bayan kasar ta samu 'yancin kanta kafin shekaru 30 da suka wuce.
Shugabannin kasashe fiye da 10, da wakilai na kungiyoyin MDD da AU da EU, da jakadun kasashe dabam daban da ke kasar Mozambique, da kuma jama'ar birnin Maputo kimanin dubu 10 sun shiga bikin nuna mubaya'a ga sabon shugaban kasa. (Bello)
|